Yan adawa a Lebanon sunyi kira da gaggauta Zabe | Labarai | DW | 18.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan adawa a Lebanon sunyi kira da gaggauta Zabe

Yan adawa a kasar Lebanon karkashin kungiyar Hezbolah sunyi kira ga gudanar da zabe a kokarin kawo karshen rikicin siyasa na kasar.

Wannan kuwa yazo ne,bayan da gwamnatin kasar dake da goyon bayan kasashen yamma ta Firamiista Fouad Siniora taki amincewa da kafa sabuwar gwamnatin hadaka.

Tun ranar daya ga watan disamba ne magoya bayan jamiyar adawa suka fara gudanar da wata zanga zanga suna masu barazanar kifar da gwamnati wacce suke ganin bata da karfi tun murabushin da wasu ministoci masu goyon bayan Syria sukayi a makon daya gabata.

A makon daya gabata a birnin Beirut shugaban kungiyar kasashen larabawa Amr Moussa tun farko yayi ta kokarin samarda maslaha tsakanin bangarorin biyu,amma babu wata nasara ta azo a gani daya samu.