′Yan adawa a Chadi sun yi watsi da sakamakon zaɓe | Siyasa | DW | 22.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan adawa a Chadi sun yi watsi da sakamakon zaɓe

Bayan bayyana sakamakon zaɓe shugaban Chadi ''yan adawa sun kira taron gaggawa domin yin nazarin al'amarin inda suka yi watsi da sakamakon zaɓen da shugaban ƙasa da shugaba Idriss Deby ya lashe.

Tschad Präsident Idriss Deby

Idriss Deby Itno

Rahotanni daga birnin N'Djamena na Ƙasar Chadi na cewar ya zuwa yau babu wata alama ta tashin hankali bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta Chadi ta bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar,wanda ya bai wa shugaba mai ci Idriss Deby nasarar sake ɗarewa kan mulkin ƙasar da kishi 61,56 cikin 100. yayin da mai bi masa Saleh Kebzabo da ke a matsayin madugun 'yan adawar ƙasar ke da kishi 12,80 cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa.

'Yan adawar sun kira taron gaggawa domin ƙalubalatar sakamakon

Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar

Saleh Kebzab tare da Ngarlejy Yorongar dukkaninsu shugabannin 'yan adawa

Daga daran Alhamis zuwa Jumma'a magoya bayan jam'iyya mai mulki ta MPS sun yi ta harbi sama da bindigogi domin nuna murnarsu na lashe zaɓen. Jim ka'dan dai bayan sakamakon Shugaba Idriss Deby ya yi jawabi a gaban magoya bayansa.

" Ku nuna murnarku ta wannan nasara da muka samu ta wuccin gadi, cikin nitsiwa ba tare da cika tituna ba, ku yi jira a hankali lokaci na zuwa inda za mu gudanar da babban biki.''Tuni dai 'yan adawan ƙasar ta Chadi suka kira wani taron gaggawa a wannan Jumma'a domin sanar da matsayinsu kan wannan sakamo, wanda tun farko suka ce ba za su aminta da shi ba.

Sauti da bidiyo akan labarin