An yi turereniyar a wani filin kwallo da ke a wajen birnin Monrovia a yayin wani taron addu'a da aka fi sani da ''crusade'' a Laberiyar.
Wani turmutsitsin mabiya addinin Kirista a Laberiya ya yi ajalin mutane akalla 29. Kafofin yada labaran kasar sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba wayar garin Alhamis din nan.
Kawo yanzu babu cikakken bayani a kan yadda yamutsin ya yi sanadiyyar mutuwar masu ibadar. To amma 'yan sanda sun ce akwai yiwuwar adadin mutanen da lamarin ya halaka sun haura 29.