1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida

October 30, 2023

Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da suka mutu ya kai 8,306

https://p.dw.com/p/4YCX6
Gazastreifen Israel Krieg mit Hamas
Hoto: Maya Alleruzzo/AP Photo/picture alliance

Isra'ila na ci gaba da tsaurara hare-hare ba kakkautawa a Arewacin Gaza ta sama da kasa, kusa da wani asbibiti da dubban Falasdinawa suka nemi mafaka, musamman ma wadanda suke dauke da raunuka.

Karin bayaniSojin Isra'ila sun tsananta luguden wuta a Gaza

Sojin Isra'ilar sun ce sun far wa sansanoni kusan 600 na mayakan Hamas, tare da kashe da dama daga cikinsu, tun bayan tsaurara hare-haren daga juma'a zuwa yau Litinin.

Karin bayanSojojin Isra'ila sun kutsa Zirin Gaza ta kasai

Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da suka mutu ya kai 8,306, cikinsu har kananan yara 3,457, sai mata 2,136, inda a jiya Lahadi kadai aka kashe mutane 304, wadanda suka jikkata baki-daya kuma sun kai 21,048. Haka zalika akwai wasu 1,950 da suke karkashin baraguzan gine-gine har yanzu.