Yakin Aleppo ya killace kimanin mutane miliyan daya | Labarai | DW | 22.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin Aleppo ya killace kimanin mutane miliyan daya

MDD ta ce adadin mutanen da yaki ya rutsa da su a yanayin yinwa da rashin magunguna a birnin na kasdar Siriya da kewayensa yasa dimbin jama cikin kuncin rayuwa

Sai dai babban jami‘in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O‘Brien, ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar a wannan Litinin cewa  a yanzu adadin mutanen da yakin ya ritsa da su a birnin na Aleppo da kewayensa ya tashi daga kusan mutun dubu 400 a baya zuwa miliyan daya a halin yanzu.

Kuma ya zargi mahukuntan Siriyar da daukar matakin barin mutanen a cikin yunwa da haramta kai masu duk wani dauki ko agaji domin tilasta masu tserewa daga gidajensu.