Yaki na kara yin muni a Raqqa | Labarai | DW | 24.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki na kara yin muni a Raqqa

Kungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty International ta ba da rahoton cewar dubban fararan hula sun makale a garin Raqqa na Siriya cibiyar mayakan Kungiyar IS

Majalisar Dinkin Diuniya ta ce akwai mutane kamar dubu 25 a birnin na Raqqa yayin da wasu dubbai suka yi kasada suka arce duk da ruwan wutar da ake yi. Tun lokacin da dakarun FDS suka fara kai farmaki a kan Kungiyar ta IS a cikin watan Yuni da ya gabata, sun kwaci kusan kishi 60 cikin dari na yankunan da kungiyar take da iko da su tun a shekar ta 2014 a Siriya.