1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da wariyar launin fata a firimiya Lig

Gazali Abdou Tasawa MNA
April 19, 2019

'Yan wasan kwallon kafa na firimiya Lig a Birtaniya da takwarorinsu na Wales sun kaurace wa amfani da shafukan sada zumunta a wannan Juma'a a wani mataki na yaki da akidar kyama da wariyar launin fata a kwallon kafa.

https://p.dw.com/p/3H6Pa
Champions League Manchester City - Tottenham Hotspur Ilkay Gündogan
Hoto: Getty Images/M. Atkins

'Yan wasan kwallon kafa na firimiya Lig a Birtaniya da takwarorinsu na kasar Wales sun kaurace wa amfani da shafukan sada zumunta a wannan Juma'a a wani mataki na yaki da akidar kyama da wariyar launin fata da ke yaduwa sannun a hankali a filayen kwallon kafa da a saman shafukan sada zumunta a kasashen Birtaniya da Wales. 

Kungiyar kare hakkin 'yan wasan kwallon kafa a Ingila da Wales ne suka kaddamar da wannan yajin amfani da shfukan sada zumunta na zamani da suka yi wa lakabin Enough wato ya " "abun ya isa" domin jan hankalin shugabannin hukumar kwallon kafa ta duniya kan su dauki mataki wajen dakatar da wannan tabi'a ta nuna wariyar launin fata ga wasu 'yan wasa da ke kara kamari a duniyar kwallon kafa. 

Kungiyar ta bayyana matakin kaurace wa shafukan sada zumuntan na wannan karo da tsanin farko na wani gagarimin kampe na yaki da wariyar launin fata a duniyar kwallon kafa. Manyan 'yan wasan firimiya lig irin su Raheem Sterling da Man City da Harry Kane na Tottenham na daga cikin wadanda suka yi biyayya ga matakin kaurace wa mafani da shafukan sada zumunta a tsawon awoyi 24 na wannan rana ta Juma'a.