1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yaki da cutar HIV mai karya gakuwar jiki a duniya

Usman Shehu Usman M. Ahiwa
December 1, 2023

Shekaru 40 ke nan da duniya ta gano kwayar cutar HIV. Abubuwa da dama sun faru a binciken da aka yi tun gano cutar. Sai dai har yanzu akwai jahilci a game da cutar.

https://p.dw.com/p/4Zh83
Hoto: Sylvain Grandadam/IMAGO

A kiyasin hukumar kula da cutar HIV ta Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka kusan mutane miliyan 39 a duniya ke dauke da kwayar cutar HIV i zuwa bara. Kiyasin ya nuna kashi 71 cikin 100 ko dai sun karya kwayar ko kuma suna da ita amma ba a iya ganinta, ko kuma dai akalla sun rage karfin da cutar ke da shi a jikinsu.

Haka ya samu bisa maganinta da suke sha, a matakin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta kayyade. Don haka yanzu rashin fahimta ne mutum ya yi tsammanin mai dauke cutar yana iya yadawa wani. A cewar Holger Wicht, kakakin kungiyar tallafa wa masu fama da cutar HIV na kasar Jamus.

"Yawancin mutane har yanzu suna ganin cewa cutar HIV AIDS ko da yaushe ana iya yadawa, watau idan mutum yana da ita. Wannan a zahiri ba haka yake ba a yanzu".

Har i zuwa yau din nan akwai masu ganin cutar HIV tatsuniya ce. Akwai ra'ayoyi da yawa wadanda ke da alaka da saka tsoro a zukatan jama'a da zarar sun ji sunan cutar. A wasu lokuta kuma tare da hukunce-hukunceirin na al‘adu. Adrian Puren, babban darakta ne a cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa a kasar Afirka ta Kudu.

"Ina ganin har yanzu akwai matakan da aka rasa, ko kuma fargabar da har yanzu akwai bukatar a magance ta, domin ina ganin akwai wasu al'umma a cikin kasashe daban-daban, musamman ma a Afirka ta Kudu. Wadanda ke da fargabar kyama idan an son suna da cutar"

Babbar hanyar kamuwa ita ce ta jini a yayin jima'i. Wannan ita ce babbar hanya. Sauran kuma su ne, alal misali wajen karin jini, idan mai dauke da kwayar cutar ya bai wa marar lafiya jini, ko kuma mutumin da ke dauke da kwayar cutar HIV ya yi amfani da misali aska aka zo aka yanki wani da shi lokacin aski misali"

Tsoron da ake yi wa cutar ga wadanda suka yarda da ita, da kuma irin tatsuniyoyi da ake ji daga wadanda ba su yarda cutar ba, na nan na cikin matsalar yada cutar HIV, domin irin wadannan halayen ba sa barin mutane su yi gwaji balle su san ko suna dauke ita ba, ta yadda za su rika shan magungunan karya karfinta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani