1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen cutar HIV\AIDS a kan kananan yara

Binta Aliyu Zurmi
February 1, 2023

Kasashen Afirka 12 sun fidda wani sabon shiri da ke da nufin kawo karshen cutar HIV\AIDS ko SIDA a kan kananan yara nan da shekarar 2030.

https://p.dw.com/p/4MzVF
Sir Alex Ferguson Flash-Galerie Iran
Hoto: AP

Sabon shirin da ke da nufin inganta yadda ake gudanar da gwaji da yadda za a kula da masu dauke da cutar da ma hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar.

Yarjejeniyar ta Dar es Salam da ta kunshi kasashen Najeriya da Angola da Kenya da Afirka ta Kudu da Uganda da Tanzaniya sun amince da kawo karshen wannan cuta a tsakanin kananan yara.

Hukumar da ke sanya idanu kan yaduwar kwayar cutar HIV AIDS ko kuma SIDA ta Majalisar Dinkin Duniya UNAIDS, ta ce kusan kaso 50 cikin dari na yaran da ke dauke da cutar ne ba sa samun magani, kuma a cikin kowane mintuna biyar a kan sami yaro daya da ke mutuwa sanadiyar wannan cuta.