Yaki da bangar siyasa tsakanin matasa | Himma dai Matasa | DW | 23.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Yaki da bangar siyasa tsakanin matasa

Wata kungiya a Jihar Katsina da ke Najeriya ta tashi tsaye wajen mayar da matasa makarantu maimakon bangar siyasa da janyo tashe-tashen hankula.

A yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina  a Najeriya wasu mutane masu kishin ganin matasa sun samu ilmin boko sun bar bangar siyasa, sun kafa wata kungiya inda suke fadakar da matasa mahimmanci ilmin boko da kuma illar bangar siyasa.

Matasa da dama dai a Jihar katsina sun mayar da bangar siyasa babbar sana'ar samun kudi inda suka bar karatun boko. A yanzu haka dai wannan kungiya ta yi nasarar mayar da matasa kusan 350 makarantun boko a yankin daga jihar ta katsina.

Alhaji Ibrahim Bala da ke zama shugaban wannan kungiya ya shaida cewa fadakar da matasa da jawosu a jika su tsinduma a harkar neman ilmi abu ne da ya rataya a wuyan kowa.

Bangar siyasa za a iya cewa ta zama ruwan dare musamman tsakanin matasan kasashen Afirka inda masu madafun iko ke amfani da su dan su cimma manufarsu daga baya su watsar da su amma babu abin da zai kankare wannan matsalar illa ilmantarwa.