1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin JTF a lokacin zabe

February 13, 2019

Duk da cewa ba su da makamai da za su sa mutane su ji tsoronsu, matasan na Civilian JTF na yin aikinsu ba sani ba sabo inda su ke kame masu laifi tare da mika su ga hukumomin tsaro don hukuntasu

https://p.dw.com/p/3DIah
Civilian JTF
Hoto: picture-alliance/AP/Abdulkareem Haruna

Akwai gungun matasa da ake kira da ECOMOG wadanda ke bin ‘yan siyasa da su nuna musu goyon bayan inda ake fargabar za su iya haifar da rudani a lokutan da ake gudanar da zabuka.

Ba dukkanin jami'an tsaro su ke iya gane irin wadan nan matasa ba saboda yadda su ka saje a cikin al'umma abin da ke zama kalubale wajen ko dai kame su ko kuma hana musu rawan gaban hantsi.

Matasan Civilian JTF dai sun taka muhimmiyar rawa wajen korar mayakan Boko Haram daga cikin kwaryar Maiduguri kuma a yanzu haka su ne su ka fi kusa da al'umma abinda ya sa ake ganin za su taimaka gaya wajen magance rikicin a lokacin zabuka musamman tsakanin matasa.

Nigeria Bürgerrechtler Ahmed Shehu
Ahmed Shehu shugaban kungiyoyin farar hula a yankin Arewa maso GabashiHoto: DW/T. Mösch

Malam Abba Aji Kalli wanda aka fi sani da Elder babban Kwamandan wannan runduna ce ta matasan Civilian JTF, ya ce su na fadakar da matasan gari har ma na cikin rundunar su na yadda za su gujewa bat agarin ‘yan siyasa da za su yi amfani da su wajen kawo rikici a zabukan da ke tafe.

To sai dai akwai masu bayyana damuwar cewa wannan runduna ganin gwamnatin jihar Borno ta dauke su aiki ta kuma biya biyan su akwai yiwuwar za yi amfanin da su wajen biyawa gwamnatin bukatar ta a lokacin zabukan.

Altine Muhammad Abdullahi daya daga cikin matan da su ka jajirce wajen yin wannan aiki ta ce su ba su goyon bayan kowane bangare a siyasar da ake yi.

Nigeria Bürgerwehr Altine Mohammed Abdullahi
Altine Mohammed AbdullahiHoto: DW/T. Mösch


Ambasada Ahmed Shehu shi ne shugaban gamayyar Kungiyoyin fararen hula na shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.
Masu fashin baki dai sun yi fatar matasa su gudanar da ayyukan su tsakani da Allah domin ayi zabe lami lafiya ba tare da nuna son kai ko goyon bayan wani dan takara ko jam’iyya ba