Yakar fashin teku a Afirka
October 27, 2013Talla
Shugabannin sun ambata hakan ne yayin da suka fara wani taro a ranar Asabar a kasar Senegal inda suka ce za su tashi tsaye wajen warware wannan matsala ta fashin teku da ma ta'addanci a yankunan.
Wannan taro na ranar Asabar dai ya biyo bayan makamancinsa da aka gudanar a kasar Kamaru a cikin watan Yunin da ya gabata wanda ya fidda wasu dabaru na yakar fashin tekun bayan da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da a yi hakan.
Fashin na teku a mashigar kogin na Gini dai na jawo asarar miliyoyin daloli ga 'yan kasuwa da ma dai gwamnatoci.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal