Yajin aiki a Nigeria | Labarai | DW | 20.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aiki a Nigeria

Rahottani daga Taraya Nigeria sun ce yajin aiki sai illah masha Allahu ,da ƙungiyoyin ƙwadago su ka fara yau ya samu karɓuwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Al´ammura sun tsaya cik, mussamman a opishin gwamnati da bankuna.

Saidai yan kasuwa a wurarre da dama, ba su amsa kira ba,, duk da cewar su na bada goyan baya ga ƙungiyar ƙwadagon ta NLC.

Kakakin ƙungiyar NLC Owei Lafemka, ya bayyana gamsuwa a game da nasara da su ka cimma, ya kuma ce za su ci gaba da tantanawa da gwamnati domin samin mafita.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa Abdul Wahid Umar ya bayyana wa sashen haussa na Redio DW bukatocin da su ka gabatar ga gwamnatin Taraya.