1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yahya Jammeh ya kame sojoji da farar hula

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 2, 2015

Gwamnatin Gambiya ta cafke wadanda take zargi da marar hannu a yunkurin juyin mulki bisa zargin goyon bayan ketare don gudanar da ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1EE5Q
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Hukumomin Gambiya sun cafke mutane da dama cikin har da fararen hula da ake zargi da marar hannu a manakisar yunkurin juyin mulki da ya ci tura a farkon wannan makon. Gwamnatin Yahya Jammeh ta bayyana cewa tana da kwararan shaidu dake nuna cewar manyan kasashen ketare na da hannu a wannan yunkuri. Hukumar leken asirin kasar ta ce ta gano jibgin makamai da kuma gurneti a tashar jirgin ruwan kasar, wadanda za a iya amfani da su wajen hambarar da gwamnati.

Sai dai kuma a cikin jawabinsa na karshen shekara, shugaba Yahya Jammeh na Gambiya ya musanta cewar an yi niyar yi masa juyin mulki. Amma kuma ya danganta abin da ya faru da ayyukan ta'adanci dake samun goyon bayan kasashen Amirka da Jamus da kuma Ingila.

Tuni dai gwamnatin Amirka ta wanke kanta daga zargin da ake yi mata, inda am'aikatar harkokin wajenta ta ce ba ta hannu a lamarin da ya auku a birnin Banjul. Wasu sojoji dake bore ne suka shafe sa'o'i suna harbe-harbe a ranar Talata da ta gabata a fadar shugaban kasa, a lokacin da shugaban kasa Yahya Jammeh yake ziyarar a ketare