Yahya Jammeh ya amince ya mika mulki. | Siyasa | DW | 20.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yahya Jammeh ya amince ya mika mulki.

Bayan jayayya ta tsawon lokaci da kuma matakai na diplomasiyya daga shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afirka, a karshe Yahya jammeh ya amince zai sauka ya mika mulki ga sabon shugaba Adama barrow.

Yahya jammeh wanda ya dade yana mulkin Gambiya ya amince zai mika mulki da kuma barin Gambiya domin yin hijira zuwa wata kasa.

Mai Ahmad Fatty wani na hannun daman sabon shugaban kasar Adama Barrow ya baiyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Tun da farko wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace tattaunawar sulhu da ake yi da Yahya Jammeh ta yi armashi.

Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun yi ta ganawa da Yahya Jammeh wanda ya sha kaye a zabe domin jan hankalinsa ya rungumi kaddamar ya sauka ya mika mulki ga shugaban da aka rantsar Adama Barrow.

Tuni dai sojojin kasashen na yammacin Afirka suka kasance cikin shirin ko ta kwana na amfani da karfin soji idan tattaunawar ta ci tura.