Yahouza dan jarida ne kana dan siyasa a Jamhuriyar Nijar.
Bisa ga yadda ya shaida, tun yana dan makaranta ya fara harkokin siyasa daga bisani kuma ya shiga aikin jarida har ma ya yi aiki da Sashen Hausa na DW na tsawon lokaci. Daga DW din ne aka nada shi matsayin minista a gwamnatin Shugaba Issoufou Mahamadou.