Ya kamata Burundi ta dage zabe | Siyasa | DW | 07.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ya kamata Burundi ta dage zabe

Shugabannin kasashen yankin Gabashin Afirka na kira ga Burundi ta dage zaben shugaban kasar daga watan Yuli sakamakon rikicin kasar.

Yoweri Museveni

Museveni na Uganda ne mai shiga tsakani a rikicin Burundi

Shugabannin na Kungiyar kasahen EAC sun cimma wannan matsaya ne ranar Litinin a taron koli karo na uku da suka yi a birnin Dar Es Salam na Tanzaniya, inda suka tattauna batun samar da hanyoyin kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Burundi a sakamakon dagewa da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi na tsayawa takara a wa'adi na uku na zaben shugaban kasa. Dr. Richard Tsezibera shi ne babban sakatare na Kungiyar ta EAC:

"Taron ya nada shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni a matsayin mai shiga tsakani, domin sassanta bangarorin da ke rikici da juna a Burundi a kan maganar zabubukan, sannan kuma ya ce taron ya tanadi a la dole a kwance dammarar mayakan sa-kai na Kungiyar, Imbonerakure da ke goyon bayan shugaban kasar na Burundi da kuma wasu sauran kungiyoyi"

Burundi ta goyi bayan shawarwarin da taron ya dauka

Taron wanda shugabannin kasashen Tanzaniya Jakaya Kikwete da na Yunganda Yoweri Museveni kawai suka halarta, daga cikin shugabannin yankin ana nuna gamsuwa ga nasarorin da aka cimma, kuma ko-da-shi- ke shugaban na Burundi bai halarci taron ba, wakilinsa ministan harkokin waje Aime Alain Nyamitwe ya ce

Konferenz in Kampala

A wannan karon dai ba duka shugabannin suka halarci taron ba.

shawarwarin da aka amince da su a taron sun yi daidai kana ya jaddada cewar gwamanatinsu za ta yi nazarin bukantu na Kungiyar ta EAC. To sai dai a bangaran 'yan adawar na kasar ta Burundi, ana ganin matakan da kasahen na yankin gabashin Afirka suka dauka ba su isa ba, inji Agathon Rwasa wani jigo daga jam'iyyun siyasar da ke hamayya da takarar shugaba Nkurunziza

"Babu dai alamun daukar mataki mai tsauri da shugabannin suka yi a kan hukumomin na Burundi, domin ko kadan ba su kawo maganar zabubukan da aka gudanar a kasar ba a makon jiya ya ce ga shi nan sun shirya zaben su kadai cike da magudi, ya ce babu wani amfani da zaben yake da shi ga jamaa domin ba su zaba ba."

Sojojin da ke gudun hijira sun ce za su matsawa Nkurunziza lamba

A karon farko dai tun bayan yunukurin juyin mulkin da wasu sojojin suka yim, wanda y ci tura, daya daga cikin hafsoshin sojin kasar dake yin gudun hijira a Kenya ya yi hira da wani gidan telbijin wanda a ciki ya bayyana cewar suna da hadin baki da wasu janar-janar a Burundi, a yunukrin juyin mulkin da suka yi, wanda bai samu nasara ba, wanda kuma ya jaddada cewar za su ci gaba da tayarwa gwamnatin ta Pierre Nkunrunziza hankali har sai ya sauka daga mulki, kana kuma ya ce suna da hannu a hare-haren da ake kai wa a baya-baya nan a Burundi

Tun lokacin da aka fara tashin hankalin dai a Burundi, sama da mutane guda 70 suka mutu yayin da wasu sama da dubu 140 suka ficce daga matsugunasu zuwa kasashe makobta irinsu Rwanda da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, da Tanzaniya.

Sauti da bidiyo akan labarin