Ya kamata a sake farfado da shirin wanzar da zamana lafiya a GTT ba da jimawa ba | Labarai | DW | 21.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ya kamata a sake farfado da shirin wanzar da zamana lafiya a GTT ba da jimawa ba

Jamus da Rasha sun yi kira da a gaggauta sake farfado da shirin wanzar da zaman lafiyar yankin GTT. Ya kamata bangarorin nan 4 dake shawarta batun GTT, su koma kan teburin shawarwari a cikin watan janeru, inji ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier yayin ganawarsa da takwaransa na Rasha a birnin Mosko Sergei Lavrov. Dukkan mutanen biyu sun nuna damuwa game da rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin Falasdinawa. To sai dai sabanin kiran da aka yi da ya tabo batun kare hakkin ´yan Adam a wannan tattaunawa, Steinmeier bai ce uffan ba.