1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ya ake satar bayanai ta Internet

Ramatu Garba Baba
May 8, 2018

A wannan makon mun amsa tambayoyi kan satar sirri jama'a a shafukan sada zumunta da kuma tarihin Zuwaira Shagari

https://p.dw.com/p/2xMu8

Yayin da ake kara samun rahotannin satar bayanai ta shafukan sada zumunta kamar Facebook da sauransu, mun samu tambayoyi wadanda muka mikawa masani, wanda za ku iya sauraron sautin. Shin ta yaya masu wannan aika-aikar suke samun damar yi wa mutum kutse? Wane mataki ya dace mutum ya bi domin ganin ya kare shafinsa daga masu kutsen?

Sai kuma tarihin mawakiyar nan Zuwaira Shehu Shagari, wacce fitacciya ce da ta ke yi wa DW Hausa wakoki. Kana da amasa tambayar shin ko me ake nufi da kuli-kulin Kubura? Ko wa ce ce Kuburan?