1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobarar daji na barna a Aljeriya

Abdul-raheem Hassan
August 12, 2021

Gobarar jeji ta mamaye arewacin kasar Aljeriya, yayin da kasar ke gudanar da zaman makoki ga mutanen da suka mutu bayan barkewar sabuwar gobarar daji da ta mamaye tekun Bahar Rum.

https://p.dw.com/p/3yvDo
Waldbrände in Algerien
Hoto: Abdelaziz Boumzar/REUTERS

Kasar Aljeriya da ke arewacin Afirka tana fama da mummunar gobarar wuta tun ranar Litinin da ta gabata, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 69, fararen hula 41 da sojoji 28.

Yanzu haka sojoji da masu aikin sa-kai na farar hula sun shiga aikin kashe gobara da ta kunno kai sakamakon yanayin iska mai karfi, an kuma kwashe mazauna kauyuka da dama don kaucewa barazanar konewa.