1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Yaushe za a kawo karshen corona?

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 19, 2022

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta nunar da cewa akwai yiwuwar annobar coronavirus da ta tashi hankalin duniya baki daya ta kawo karshe cikin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/45jNN
Berlin, Jamus | Michael Ryan | Yayin bude cibiyar binciken annobar duniya da ta cikin gida
Dakta Michael Ryan babban darakatan kai daukin kiwon lafiya na gaggauwa na WHOHoto: Eventpress SK/picture alliance

Babban daraktan kai daukin kiwon lafiya na gaggauwa a hukumar ta WHO Dakta Michael Ryan ne ya bayyana hakan, sai dai ya ce wannan ba ya nufin annobar za ta bace baki daya saidai ta zama cutar da ke yaduwa a cikin gida. Hakan dai na nufin cutar za ta zauna din-din-din a cikin al'umma, sai dai kuma illarta ba za ta kai ta lokacin da ta bulla ba sakamakon kariyar da jikin dan Adam ya samu daga ita. Ryan ya nunar da cewa bukatar daukin gaggawa da annobar ta haifar, zai zo karshe ta hanyar yi wa mutane da dama allurar riga-kafi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da a wasu kasashen kamar Jamus ake samun karuwar wadanda suka kamu da cutar. Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Jamus din Robert Koch Institute, ta bayyana cewa adadin wadanda ke kamuwa da cutar a kasar a kullum ya kai sama da dubu 100. Cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar, ta nunar da cewa mutane dubu 112,323 da suka kamu da corona kana mutane 239 suka riga mu gidan gaskiya a tsawon sa'o'i 24 da suka gabata. Wannan dai shi ne karon farko tun bayan barkewar annobar a duniya da aka samu mutane sama da dubu 100 sun kamu da COVID-19 din a Jamus, inda a ranar Jumma'ar makon da ya gabata kuma a karon farko mutane sama da dubu 90 suka kamu da cutar a kasar.