SiyasaJamus
WHO ta sake gargadi kan yaduwar Omicron
December 15, 2021Talla
Shugaban Hukumar ta WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce akwai kasashe 77 da cutar ke cikinsu, kuma akwai yiwuwar sun shige cikin tarin wasu kasashe da ba a iya tantance su ba har yanzu.
Omicron wanda da farko ya bulla a kasar Afirka ta Kudu, na saurin rikida abin kuma da yake kada hankalin masana kimiyyar lafiya a duniya.
Amirka wacce coronar ta yi wa lahani, na da sama da mutum dubu 800 da ta halaka a cewar cibiyar bincike da ke jami'ar Johns Hopkins ta kasar.
Sanarwar hukumar ta WHO ta zo ne daidai lokacin da kamfanin harhada magungunan na Pfizer, ya ce rigakafin da ya samar na tasiri a kan Omicron din, duk da cewa bayanan farko sun nuna akasin hakan.