1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Intanet na sa bazuwar cututtuka ta jima'i

June 7, 2019

Kafar sadarwar Intanet ta zama wata babbar barazana ga yaki da ake yi da yaduwar cututtukan da ke samuwa ta hanyar jima'i, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar.

https://p.dw.com/p/3K0MC
China Krankenhaus in Nanning, Spritze HIV
Hoto: picture-alliance/Zuma Press/Xinhua/Lu Bo'An

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana irin koma bayan da ake fuskanta ta fuskar yaki da cututtukan da ke yaduwa ta hanyar jima'i, tana mai gargadi kan karuwar manhajojin da ke kitsa hulda tsakanin maza da mata a shafukan Intanet.

Sama da mutum miliyan guda ne ke kamuwa da cutukan na jima'i a kowace rana a duniya, inda ake samun akalla mutum guda cikin mutum 25 da ke kamuwa da wani nau'i na cutar.

Ta nuna damuwa da yadda mutane suka mayar da jima'i a rayuwar yau, da ma ake iya samu a sawwake ta hanyoyin na Intanet.

Hukumar ta dai danganta yin watsi da matakan kariya da masu dabi'ar ke yi da kasancewa cikin dalilian karuwar matsalar a fadin duniya.