WHO: Ebola ta barke a Jamhuriyar Kwango | Labarai | DW | 12.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO: Ebola ta barke a Jamhuriyar Kwango

Barkewar annobar Ebola da aka samu ta karshe a Kwango a shekarar 2014 ta yi sanadi na rayukan mutane 49.

Annobar Ebola ta barke a Arewa maso Gabashin Dimukaradiyyar Kwango kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a wannan rana ta Juma'a, mutane uku ne dai aka tabbatar da mutuwarsu ta sanadin wannan cuta tun daga ranar 22 ga watan Afirilu.

A cewar Hukumar WHO dajin nan na lardin Bas-Uele da ya yi iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya shi ma a bin ya shafeshi. Barkewar annobar Ebola da aka samu ta karshe a Kwango a shekarar 2014 ta yi sanadi na rayukan mutane 49.

Ministan lafiya a kasar ta Kwango Oly Ilunga ya tabbatar da barkewar annobar ta Ebola a kasar.