1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinciNa duniya

WFP na jan hankali kan barazanar 'yunwa

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2023

Hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa matsalar rashin kudin da take fuskanta za ta iya jefa mutane miliyan 24 cikin hali na 'yunwa a kasashe da dama ciki har da Haiti da Somaliya da Siriya.

https://p.dw.com/p/4WFOR
'Yunwa na sa mutane rokon abinci a wasu sassa na SomaliyaHoto: picture alliance/abaca

Hukumar WFP da ke da mazauni a birnin Rome ta koka kan yadda ake samun karuwar bukatun abinci a duniya, yayin da take fuskantar gibin kudade na sama da kashi 60 cikin 100, wanda ke zama mafi girma a tarihinta. Hukumar ta abinci ta kara da cewa , duk wani mataki na rage kashi 1% na tallafin na barazanar jefa mutane 400,000 cikin halin rashin abinci.

Karin bayani: karancin abinci ya sa Nijar

Kiyasi ya nunar da cewa mutane miliyan 40 na fuskantar matsalar yunwa a kasashen Afghanistan da Siriya da Somaliya da Haiti sakamakon tsuke bakin aljuhu da WFP ta yi.