Weah zai karbi madafun iko a Laberiya | Labarai | DW | 22.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Weah zai karbi madafun iko a Laberiya

A wannan Litinin din ake rantsar da tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah a matsayin sabon shugaban kasar Laberiya.

A wannan Litinin din George Weah tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya zai karbi madafun iko a mastayin shugaban kasar Laberiya, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a watan jiya, a kasar ta yammacin Afirka.

Weah mai shekaru 51 da haihuwa zai karbi madafun iko daga hannu Ellen Johnson Sirleaf wadda ta mulki kasar na tsawon shekaru 12 kuma ta ke zama mace ta farko da aka zaba domin ta jagoranci wata kasa da ke nahiyar Afirka.

Sabon shugaban yana da jan-aiki na farfado da tattalin arzikin kasar wadda ke cikin mawuyacin hali musamman bayan cutar Ebola da ta tagayyara kasar gami da cin hanci da rashawa da suka yi katutu tsakanin manyan jami'an gwamnati.