Wata kotu a Chadi na zaman yin shari'a na tsofin jami'an gwamnatin Hissene Habre
November 14, 2014Talla
Ana dai zargin mutanen ne da haɗin baki da tsohon shugaban ƙasar Hissene Habre,wajen aikata kisa da azabtar da jama'a a lokacin mulkinsa daga shekaru 1982 zuwa shekarun 1990.
Daga cikin waɗanda suka gurfana a gaban kotun har'da Mahamat Djibrine tsohon shugaban hukumar bincike na ƙasar da kuma wasu sauran jami'an na hukumar leƙen asiri. Tshohon shugaban na Chadi wanda aka yi wa juyin mulki a shekarun 1990 ana zarginsa da akaita kisan gilLa a kan wasu daruruwan mutane.