Wasu mutane sun kai hari a majalisar dokokin Libiya | Labarai | DW | 18.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu mutane sun kai hari a majalisar dokokin Libiya

Kasar Libiya ta fada cikin rudun siyasa, inda wasu sojoji da ke biyayya ga tsofon Janar din soja na Libiya Khalifa Haftar, sun ayyana kansu a matsayin sojojin kasar ta Libiya na sahihi

A cewar Mohamed Al-Hedjazi, kakakin kungiyar ANL da tsofon Janar din sojan na Libiya ya kafa, su ne a matsayin su na sojan kasar Libiya suka mamaye majalisar dokokin.

Kanfanin dillancin labaran kasar ta Libiya LANA yace, mutane dauke da makamai sun toshe hanyar da ke zuwa ga majalisar dokokin kasar a Tripoli, inda ake iya hangen hayaki na tashi, tare da jin karan harbe-harbe a anguwanni da dama na Tripoli babban birnin kasar.

A cewar wani dan majalisa Omar Buchah, mutane dauke da manyan makammai ne, suka kai hari a ofisoshin majalisar inda suka bamka masa wuta.

A ranar Juma'a da ta gabata, dai fadan da ya barke tsakanin dakarun dake biyayya ga tsofon Janar din, da masu kishin Islama a Benhgazi ya yi sanadiyar mutuwar mutane 70.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman