1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Wasanni neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2022

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
October 11, 2021

A shirin na wannan lokaci za mu ji inda aka kwana a wasannin neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya wato World Cup. Akwai wasan sarrafa doki a Iraki da sauran wasanni.

https://p.dw.com/p/41Xc4
Nations League Finale Frankreich Spanien
Hoto: Luca Bruno/AP Photo/picture alliance

Bari mu fara da gasar kasashen Turai na Nations League da aka fafata wasan karshe a ranar Lahadi, inda Faransa da ke rike da kambun kofin kwallon kafa na duniya ta lallasa Spain da ci biyu da daya. 'Yan wasan Faransan Kareem Benzema da Kylian Mbappe ne suka zurawa Faransan kwallayen da suka ba ta damar samun wannan nasara, wacce kuma ta sanya Faransan zama zakara bayan ta sha fama a zagaye na farko na wasan da Spain ta yi kaka gida.

A karshen makon an ci gaba da fafatawa a wasannin neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya wato World Cup da za a fafata a kasar Qatar. A nahiyar Turai dai kasashen Ingila da Scotland da Sabiya da Sweden da Switzerland da kuma Ukraine sun taka rawar gani a wasannin da suka fafata. A wasannin da aka yi a ranar Jumma'a dai, an tashi wasa canjaras biyu da biyu tsakanin Jamhuriyar Cek da Wales, Netherlands ta lallasa Latvia da ci daya mai ban haushi, Turkiyya da Norway sun tashi kunnen doki daya da daya kana an tashi wasa Jamus na da ci biyu Romaniya na da daya. A wasannin ranar Asabar kuwa, Sweden ta lallasa Kosovo da ci uku da nema, Girka ta lallasa Jojiya da ci biyu da nema Denmark ta caskara Maldova da ci hudu da nema kana Ingila ta yi wa Andora cin kaca da ci biyar da nema.

Murnar cin kwallo a fafatawa tsakanin Jamus da Romaniya, inda aka tashi Jamus 2 Romaniya 1
Murnar cin kwallo a fafatawa tsakanin Jamus da Romaniya, inda aka tashi Jamus 2 Romaniya 1Hoto: Martin Rose/Getty Images

Bayan kashi da ta sha a wasanni  biyu cikin ukun da ta buga, Japan na bukatar zage damtse kafin ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. Hakan na nufin tilas Japan ta doke Ostiraliya a fafatawarsu ta ranar Talatar wannan makon. In har hakan ba ta samu ba, Japan din za ta gaza halartar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a karon farko, tun daga shekara ta 1994. A Alhamis din makon da ya gabata dai, Japan din ta sha kashi a birnin Jeddah a karawarsu da Saudiyya da ci daya mai ban haushi. Tuni dai 'yan wasan na Ostiraliya suka isa Japan cike da kwarin gwiwa. Yayin da Japan din za ta karbi bakuncin Ostiraliya, Saudiyya za ta fafata da Chaina kana Iran za ta karbi bakuncin Koriya ta Kudu.

Amirka ta sha kashi a hannun Panama da ci daya mai ban haushi, yayin da aka tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Jamaika da Kanada. Costa Rica ta lallasa El Salvador da ci biyu da daya yayin da Mexico ta caskara Honduras da ci uku da nema. A Larabar wannan makon za a fafata tsakanin Amirka da Costa Rica kana Kanada ta karbi bakuncin Panama, Jamaika kuma za ta yi tattaki zuwa Honduras, ita kuwa El Salvador ta karbi bakuncin Mexico.

Lokacin da Choupo-Moting (dama) ya ci wa Kamaru kwallo a fafatawa tsakanin Kamaru da Mozambik a birnin Douala
Lokacin da Choupo-Moting (dama) ya ci wa Kamaru kwallo a fafatawa tsakanin Kamaru da Mozambik a birnin Douala Hoto: Beloumou Olomo/AFP

Idan muka koma gida Afirka kuwa, Nijar ta sha kashi a hannun Aljeriya ta ci shida da daya kana Burkina Faso ta lallasa Djibouti a gida da ci hudu da nema. An tashi wasa tsakanin Zambiya da Equatorial Guinea kunnen doki daya da daya, kana bayan da Najeriya ta yi abin kunya wajen shan kashi a gida da ci daya da nema a wasanta da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a ranar Alhamis din da ta gabata, ta farfado inda ta rama cin ta kuma kara a Lahadin karshen mako ta hanyar bin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar har gida, ta kuma lallasa ta da ci biyu da nema. Mali ma ta bi Kenya har gida ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi kana Afirka ta Kudu ma ta bi Habasha har gida ta caskara ta da ci uku da daya.

Masu wasan iya sarrafa doki na kasa a Iraki sun dawo filin daga bayan shekaru 10 da kaurace mata. Ana dai wasan sarrafa doki a kasar ne duk shekara.

Shararren dan wasan dambe na ajin masu nauyi Tyson Fury ya ci gaba da rike kambunsa, bayan kisan da ya yi wa Deontay Wilder a turmi na sha daya. Fafatawa ce dai mai tsaurin gaske fiye da yadda aka yi hasashe, sai dai dan damben Birtaniyan Fury ya lallasa takwaransa Wilder na Amirka, abin da ya sanya shi kara zama gagara-badau a harkar damben ajin masu nauyi.