1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Murna ta koma ciki ga Schalke 04

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 18, 2021

A cikin shirin za a ji cewar murna ta koma ciki ga magoya bayan kungiyar Shalke 04 ta Jamus. An bude gasar cin kofin Afirka na matasa masu taka leda a gida karo na shida a karshen mako a Kamaru.

https://p.dw.com/p/3o59H
Fußball Bundesliga | Eintracht Frankfurt - FC Schalke | Luka Jovic
Hoto: Kai Pfaffenbach/AFP/Getty Images

Za mu fara da gasar kwallon hannu ta duniya ta maza da aka bude a tsakiyar makon da ya gabata a kasar Masar, inda a karshen mako aka fafata a zagaye na biyu na gasar. A ranar Lahadi dai, an tashi wasa canjaras 32 da 32 tsakanin Tunisiya da Brazil, haka kuma an tashi wasa tsakanin Poland da Spain, inda Spain din ta samu nasara da 27 da 26. Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango kuwa ta sha bugun kawo wuka ne a wasan da suka fafata da Denmark, inda aka tashai wasa 19 da 39 haka abin yake ga takwararta ta Yurugai inda Hangari ta lallasa ta da ci 44 da 18. Koda a wasanta na farko da ta fafata da Jamus, Yurugai din ba ta ji da dadi ba, domin kuwa an tashi wasan 43 da 14. Ita kuwa Masar da ke zaman mai masaukin baki, za a iya cewa ta shiga gasar da kafar dama, domin kuwa a wasanta na farko ta lallasa Chile da ci 35 da 29 kana a wasanta na biyu ta samu nasara a kan Macedonia da ci 38 da 19,

Bundesliga I Bayern Muenchen v  Freiburg
Wasa tsakanin Bayern Munchen da FreiburgHoto: Lukas Barth-Tuttas/REUTERS

A nahiyar Turai a karshen mako kungiyar Shalke 04 ta sake komawa gidan jiya, bayan da ta sha kaye a hannun Frankfurt da ci 3-1 Ita kuwa Bayern ta sake matsa kaimi ne wajen ganin ta ci gaba da zama gagara-badau a saman tebur, inda ta lallasa Freiburg da ci 2-1 daya a wasan da suka fafata a ranar Lahadin. A wasan da aka fafata kuwa a ranar Jumma’a Unioin Berlin ta lallasa Leverkusen da ci  1-0 mai ban haushi, yayin da a ranar Asabar, aka tashi wasa kunne doki tsakanin Borussia Dortmund da Mainz daya da daya, Hoffenheim da Armenia Bielefeld  kuwa aka tashi canjaras 0-0 babu ci, haka kuma abin ya kasance tsakanin FC Köln da Hartha Berlin. Werde Bremen ta samu nasara a kan Augsburg da ci 2-0 Stuttgart da Borussia Mönchengladbach an tashi wasa ba kare bin damo 2-2 hakan ce kuma ta kasance a fafatawar da aka yi tsakanin VfL Wolfsburg da RB Leipzig. Shi ne kuma wasan da sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye.

A yanzu dai Bayern Munich ce ke kan gaba da maki 36, sai RB Leipzig da ke biye mata da maki 33 Leverkusen da Borussia Dortmund na biye mata a matsayi na uku da na hudu da maki 29 kowaccensu, sai kuma Unioin Berlin a matsayi na biyar da maki 28, yayin da tuni shalke ta sake komawa matsayinta na karshe da maki bakwai.   

UK Timothy Fosu-Mensah
Timothy Fosu-Mensah dan wasan Manchester UnitedHoto: Darren Staples/Sportimage/imago images

A gasar premier league ta kasar Ingila, a karshen mako, an tashi canjaras babu ci a fafatawa tsakanin Manchester United da Leverpool, inda Manchester United din ta ci gaba da rike kanbunta na saman tebur. Manchester City kuwa ta yi wa Crystal Palace cin kaca, ci hudu da nema Lecester City ma ta lallasa Southhampton da ci biyu da nema, inda Chalsea ta bi Fulham har gida ta yi mata ci daya mai ban haushi. A yanzu dai Manchester United na saman tebur da maki 37, yayin da takwararta Manchester City da  Lecester City ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 35, inda Leverpool ke matsayi na hudu da maki 34 sai kuma Tottenham a matsayi na biyar da maki 33.