1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Karshen kakar Bundesliga ta 2026

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 18, 2026

An kammala kakar Bundesliga ta Jamus ta bana, inda Bayern Munich ta sake zaama zakara. Sai dai akwai wasu kungiyoyi da wasansu ya fi daukar hankali a musamman a wasan karshe da aka fafata a karshen mako

https://p.dw.com/p/5DvdU
Kalubalen gasar kwallon kafa ta duniya ta 2026
Hoto: Li Muzi/Xinhua/IMAGO

Za mu mayar da hankali ne kacokam a kan kammala kakar wasannin Bundesliga ta bana a Jamus. Amma ba ri mu fara da irin kalubalen da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta bana ka iya fuskanta. A dai-dai wannan lokaci da wasu biranen Amurka suke haramar karbar bakuncin gasar da za a fara daga 11 ga watan Yuni na 2026 da hadin-gwiwar kasashen Mexico da Kanada da Amurkan, matsalar samun visa wato takardar izinin shiga kasar Amurka ga 'yan kallo tana ci gaba da yin tasiri ga tagomashin gasar. Hakan yana shafar otel-otel din da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta kama.

Yanzu bari mu dawo nan Jamus, a yayin da aka kammala kakar Bundesliga ta bana kungiyoyin Heidenheim da St. Pauli sun yi bankwana da rukuni na farko. Wasu kungiyoyin kuwa sun samu damar hayewa rukuni na frko na gasar.

Gasar Bundesligar Jamus
Gasar Bundesligar JamusHoto: Robin Rudel/Pressefoto Rudel/picture alliance

To da yake a karshen makon ne aka kammala kakar ta bana, akwai kungiyoyin da suka sha da kyar wajen samun nasarar shiga gasannin da za a yi a Turai.

Yayin da Hoffenheim ta hakura ta bar wa Stuttgart kambu na hudu bayan ta sha dan karen kashi a gidan Borussia Mönchengladbach da ci hudu da nema. Leverkussen ma ta sha da kyar, bayan da ta kammala kakar ta bana a matsayi na shida. Sai dai a bana babu damar taka rawa a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. Ita kuwa Stuttgart ta yi canjaras biyu da biyu da Frankfurt abin da ya hana Frankfurt din samun damar buga kowacce irin gasa ta Turai a bana. Wannan wasan ne ma dai sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye a karshen mako. 

Karawar Manchester City da Arsenal
Gasar Bundesligar JamusHoto: Dave Thompson/AP Photo/picture alliance

Yayin da wasanni biyu rak suka rage a kammala kakar Premier League ta Ingila ta bana, har yanzu tana kasa tana dabo ga kungiyar Arsenal da ke fatan ganin ta daga kofi a bana. Maki biyu ne dai rak tsakaninta da Manchester City da ke a matsayi na biyu, abin da ke nuni da cewa tilas Arsenal ta lashe wasanninta biyu da ke tafe kafin ta cimma burinta. A nata bangaren Manchester City ta wasa wukarta, domin kuwa tana ganin akwai yiwuwar ta sake lashe gasar ta Premier League in har Arsenal ta yi wa kanta sagegeduwa. Yanzu dai kallo ya koma sama, inda magoya baya ke dakon ganin Arsenal ta karya kofin nan na barar da damarta ta zama zakara abokan hamayya kuma ke tunanin za ta maimaita abin da ta saba.