1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin Turai

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 17, 2020

A wannan mako za mu mayar da hankali kacokam kan wasannin cin kofunan Turai na kwallon kafa wato Champions League da kuma Europa Lig da suka kai matakin kusa da na karshe.

https://p.dw.com/p/3h5ch
Champions League Barcelona Bayern München Tor Müller
Hoto: Getty Images/AFP/M. Fernandez

Kungiyoyin Bundesligar kasar Jamus wato Bayern Munich da RB Leipzig da kuma takwarorinsu na Lig 1 a Faransa wato PSG da Lyon suka samu tikitin zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun Turai na wannan shekara.

Magoya bayan kungiyar Barcelona sun tarbi 'yan wasansu a cikin sowa a lokacin isowarsu a masaukinsu a birnin Lisbon bayan cin kaca na takwas da biyu da kungiyar Bayern Munich ta yi masu a wasan kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai da suka buga a ranar Juma'ar da ta gabata. Wannan dai shi ne karo na farko a tarihi da wata kungiya ke surhwa Barcelona da kwallaye takwas a jere buga da kari ba tare da wani cin panaraty ko daya ba a gasar ta zakarun Turai.

Duk da rashin sa'ar da ta yi na zurawa kanta kwallo a cikin ragarta da kanta, Kungiyar bayern Munich ta ci gaba da dakan hurhudu a kan Barcelona inda daya bayan daya ta zura mata kwallaye hudu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Thomas Müller na Bayern Munich: Gwagwarmayar neman zura kwallo a ragar Barcelona
Thomas Müller na Bayern Munich: Gwagwarmayar neman zura kwallo a ragar BarcelonaHoto: Getty Images/AFP/M. Fernandez

Ko da shi ke bayan dawowa daga hutun rabin lokacin Luis Suarez dan wasan gaba na Barcelona ya yi nasarar zura kwallo daya mai kyau, to amma wannan kwallo tasa ta zamo tamkar wani tsokalo tsuliyar dodo inda Yaya Babba ta sake fusata ta koma dakan hurhudu a kan Messi da sauran takwarorinsa da ke a matsayin 'yar galadimar gasar la Ligar kasar Spain inda ta sake zura mata kwallaye hudu wanda a jumulce suka tashi takwas da biyu, cin da wasu ma'abota kwallon kafar suka bayyana a matsayin kusan wata shirka a duniyar kwallon kafa.

Ga bisa dukkan alamu dai wannan nasara da Kungiyar Bayern Munich ta samu kan Barcelona ba Jamusawa kadai ta faranta wa da rai ba. A kasashen Afirka da dama watakila a bisa tasirin shirin Bundesliga kai tsaye na sashen Hausa, matasa da dama ne suka nuna farin cikinsu da nasara ta Bayern.

Karawa tsakanin RB Leipzig ta Jamus da Atletico Madrid ta Spain
Karawa tsakanin RB Leipzig ta Jamus da Atletico Madrid ta SpainHoto: picture-alliance/dpa/P.Schatz

Ko baya ga Bayern Munich Kungiyar RB Leipzig ta kasar ta Jamus ta yi nasarar samun tikitin zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turan, bayan ta doke Atletico Madrid ta kasar Spain da ci biyu da daya. Lamarin da ya bai wa kungiyar ta Leipzig da matashin mai horas da 'yan wasanta Julian Nagelsmann damar kafa tarihi kaiwa a karon farko wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai. Kuma ko baya ga Kungiyoyi biyu da Jamus ta kai a wasan kusa da na karshen, a karon farko Jamus din ta kafa tarihin samar da masu horas da 'yan wasa guda uku da suka kai kungiyoyinsu a wannan matsayi wato Hans Flick na Bayern Munich, Julian Nagelsmann na Leipzig da Tomas Tuchel na PSG ta kasar Faransa.

A sauran wasannin neman tikitin zuwa wasan kusa da na karshe inda da kyar da jibin goshi ne Kungiyar PSG ta doke Atlanta Bergam ta Italiya da ci biyu da daya, kusan ba zato ba tsammani ne kuma Kungiyar Lyon ta kasar Faransa da ta kare a matsayin ta bakwai a gasar Lig 1 da ta gabata ta yi waje road da Kungiyar Man City ta Ingila, wacce ta kare a matsayin ta biyu a tebirin Premiya Lig da ci uku da daya.

'Yan wasan Olympique Lyon na taya Maxwel Cornet murnar cin kwallo a karawarsu da Manchester City
'Yan wasan Olympique Lyon na taya Maxwel Cornet murnar cin kwallo a karawarsu da Manchester CityHoto: picture-alliance/AP Photo/F. Fife

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin gasar cin kofin zakarun Turai da kungiyoyi biyu na kasar Faransa ke kaiwa wasan kusa da na karshe, inda Kungiyar PSG za ta kara da Leipzig a yayin da Bayern Munich za ta fafata da Lyon, wanda ke nufin a kwai yiwuwar a buga wasan karshe a tsakanin kungiyoyin Bundesliga idan Bayern da Leipzig suka ci wasansu ko kuma a tsakanin na Lig 1 ta kasar Faransa idan PSG da Lyon suka yi nasara. Matsayin da kungiyoyin na Bundesliga da na Lig 1 suka kai a wannan karo a gasar cin kofin zakarun Turai na a matsayin wani babban kalubale ga gasar Firimiya Lig ta Ingila da La Ligar Spain da Serie A ta Italiya wadanda ake kallo a matsayin manyan lig-lig na Turai a kan lig din Bundesligar da Lig1.

A gasar Cin karamin kofin kwallon kafa na Turai ko kuma Europa Lig  kungiyar Man United ta kwashi kashinta a hannu a gaban Sevilla ta kasar Spain, wacce ta doke ta da ci biyu da daya a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar Lahadi. A wannan Litinin ake karawa tsakanin Inter Milan ta Italiya da Chaktar ta Ukraine dan ba da damar sanin wacce za ta yi rakiyar kungiyar ta Sevilla a wasan karshe na cin karamin kofin Turan na Europa Lig.