1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin Bundesliga da gasar ninkaya ta kasashen Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
October 18, 2021

Bayern Munich ta kafa tarihin zura kwallaye hudu cikin mintuna bakwai a karawa da Leverkusen. Afirka ta Kudu ta tsere wa sa'a a gasar ninkaya ta kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/41pV4
Fußball Bundesliga | Bayer Leverkusen v Bayern München
Hoto: Uwe Kraft/imago images

A fagen Bundesliga, Bayern Munich ta yi wa Leverkusen dukan kawo wuka da ci 5-1 a gida BayArena a wasan mako na takwas, lamarin da ya bai wa Yaya-Babba damar jagorancin saman teburi da maki 19. Hasali ma dai Bayern ta yi nasarar kafa tarihi, inda ta ci kwallaye hudu cikin mintuna bakwai. Godiya ta tabbata ga Robert Lewandowski da ya ci biyu, yayin da shi ma Serge Gnabry ya zura biyu, shi kuwa Thomas Müller ya jefa na karshe. Rabon Bayern Munich ta ci kwallaye biyar tun kafin zuwa hutun rabin lokaci tun lokacin da ta yi wasa da Yaya-Karama Borussia Dortmund a cikin watan Maris 2018.

Ita ma Hoffenheim ta yi ruwan kwallaye a wasanta da FC Cologne inda ta zura kwallaye daya bayan daya har biyar ba tare da bakuwar ta rama ko da daya ba, lamarin da ya dadada ran kocin Hoffenheim Sébastien Hoeness:

"Ina tsammanin mun yi wasa mai kyau a yau, daga farko zuwa karshen wasan. Mun kasance cikin nitsuwa sosai da amfani da dabara. Kuma mun yi sa'a, lamarin da ya kawo sakamakon da kuka gani. Na yi farin ciki, saboda 'yan wasana sun nuna hadin kai da kuma musayar yawu mai yawa."

Niklas Tauer (hagu) na Mainz 05 da Donyell Malen (dama) na Dortmund a karawar kungiyoyinsu
Niklas Tauer (hagu) na Mainz 05 da Donyell Malen (dama) na Dortmund a karawar kungiyoyinsuHoto: Ina Fassbender/AFP

Sai dai Leipzig da ke zama mataimakiyar zakaran kwallon Jamus ta sake yin tuntube, inda ta tashi ci daya ko ta ina da Freiburg. Ita ma Frankfurt ta ji ba dadi a hannun Hertha Berlin ci 1-2, sai dai Union Berlin ta ragargaza Wolfsburg (2-0). Bochum ta dauki maki uku a kan Fürth. Borussia Mönchengladbach da Stuttgart sun tashi (1-1). Amma Yaya-karama Borussia Dortmund ta samu nasara a kan Mainz (3-1), kuma tana a matsayi na biyu a saman teburin Bundesliga da maki 18. Yayin da Leverkusen ta koma matsayi na uku da maki 16.

Yanzu kuma sai Premier league, inda Dan kasar Senegal Sadio Mané ya kai matsayin zura kwallo 100 a gasar kwallon kafa ta Premier a Ingila ranar Asabar a karawar da Watford ta yi da Liverpool. Hasali ma ya shiga cikin rukunin 'yan wasa kalilan da suka kai wannan matsayi, wadanda suka hada da abokin wasansa dan Masar Mohamed Salah wanda ya ci kwallonsa na 100 a watan da ya gabata, da kuma Didier Drogba na Cote d' Ivoire. Sai dai Didier Drogba na ci gaba da zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a tarihin kulob din Chelsea, inda ya ci kwallaye 104 a wasanni 250.

Sadio Mane (dama) da abokan wasansa na Liverpool
Sadio Mane (dama) da abokan wasansa na LiverpoolHoto: Attila Kisenedek/AFP

Amma inda Sadio Mané ya bambanta da sauran abokan burminsa, shi ne dan wasan na Senegal ya zura kwallaye 100 ba tare da bugun da kai sai mai tsaron gida ko daya ba, sabanin Drogba da Salah. Dan wasa daya tilo ne mai suna Ferdinand da Heskey ya yi nasarar cin kwallaye 100 ba tare da bugun fenareti ba kafin Sadio Mané.

A Afirka, an gudanar da wasan neman hayewa matakin rukuni na gasar neman cin kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar da aka fi sani da Champions League. Kungiyar Horoya ta Conakry da ke zama jagorar kwallon kafa a Guinea ta doke Stade Malien ta Mali da ci daya mai ban haushi a gumurzun da suka yi. Haka ita ma Zamalek ta Masar ta bi Tusker har gida Kenya ta kuma lallasa ta da ci daya da nema. Wannan nasarar dai ta bude wa Horaya da Zamalek kofar zuwa matakin rukuni na gasar, saboda suna bukatar yin canjaras a gida a wasan da za su yi a karshen mako domin hakarsu ta cimma ruwa.  Haka ita ma ASEC Mimosa ta Abidjan din Côte d' Ivoire wacce ta samu nasara da ci gida 3-1 a kan Belouizdad ta Aljeriya, tana sa ran hayewa mataki na gaba, idan ta kare matsayinta a gida Abidjan.

Sai dai kuma, wace ta lashe kofin zakarun Afirka sau da dama wato al- Ahly ta Masar ta yi abin fallasa inda US Gendarmerie Nationale ta Niamey ta shammace ta hanyar farke daya-dayan kwallo da Ali Maaloul ya zura mata. Kyakkyawar rawar gani da kungiyar ta Nijar ta taka ta sa hankali komawa kan zagaye na biyu na wasan da zai gudana a birnin Alkahira, inda za a tantance dan duma da kabewa. Ita ma Tout Puissant Mazembe da ke fada ana ji a fagen tamaula a Afirka tana cikin mawuyacin hali bayan da ta yi canjaras (0-0) a Amuzulu FC ta Afirka ta Kudu.

'Yar ninkayar Afirka ta Kudu Tatjana Schoenmaker a gasar Olympics ta 2020 a Tokyo
'Yar ninkayar Afirka ta Kudu Tatjana Schoenmaker a gasar Olympics ta 2020 a TokyoHoto: Jonathan Nackstrand/AFP/Getty Images

Kungiyar wasan ninkaya ta Afirka ta Kudu ta mamaye gasar zakarun Afirka da ta gudana a birnin Accra na Ghana, daga ranar 11 zuwa 17 ga Oktoban nan da muke ciki, inda ta samu jimillar lambobi 42. Yayin da Masar da Aljeriya ke biya mata baya a yawan lambobi. 'Yan ninkaya da suka ba da mamaki sune na Senegal, inda suka samu lambobi biyar, sabanin gasar ninkaya ta 2018, inda suka tashi ba tare da lamba ko daya ba. Ita kuwa Ghana mai masaukin baki fa, babu yabo babu fallasa don ta zo ne a matsayi na biyar.

'Yar damben boxing Lolita Muzeya ta Zambiya ta kasa cika burinta na zama zakaran duniya na hudu daga nahiyar Afirka a cikin daya daga cikin manyan rukunonin damben hudu na mata (IBF, WBA, WBC, WBO). A karawar da ta yi a wannan Asabar a birnin Newcastle na Ingila dai, Savannah Marshall da ke rike da kabun matsakaicin nauyi na WBO, ta samu nasara a kan Muzeya ta Zambiya, sakamakon dakatar da damben da alkalin wasan ta yi a karshen turmi na biyu. Wannan ne koma-bayan farko da 'yar damben Zambiyar ta  fuskanta a cikin gwagwarmaya 17 da ta yi a baya-bayan nan. Kasancewa har yanzu tana kan ganiyarta, Savannah Marshalll za ta iya mai da hankali kan yiwuwar tinkarar fitacciyar 'yar damben Amirka Claressa Shields, wanda ke rike da kambu uku na matsakaicin nauyi na IBF, WBA da WBC.

Dan tseren kasar Kenya Elisha Rotich mai shekaru 31 ya lashe gudun fanfalaki na birnin Paris a wannan Lahadin cikin sa'o'i biyu da mintuna 23 da dakika 23, lamarin da ya ba shi damar inganta bajimtar da dan kasar Habasha Kenenisa Bekele ya nuna a 2014  cikin sa'o'i biyu da mintun biyar dakika hudu. Wanda ya zo na biyu a Marathon din shi ne dan tseren Habasha Hailemaryam Kiros, yayin da wani dan Kenya Hillary Kipsambu ya zo a matsayi na uku.

A rukunin mata kuwa, Tigist Memuye ta Habasha ce ta lashe tseren da bai samu halartar matan da suka yi fice a wannan fanni ba. Su kuwa Yenenesh Dinkesa da Fantu Jimma dukkanin su 'yar Ethiopiya suka zo a matsayi na biyu da na uku.