Leipzig tana kan gaba a wasannin Bundesliga
September 2, 2019Talla
A wasannin Bundesliga na Jamus ta canza zane a saman tebirin na Bundesliga wanda kungiyar Leipzig ta dare da maki tara bayan a ranar Juma'a ta bi Mönchengladbach har gida ta kuma lallasata da 3-1, yayin da Bayern Münich ta taso daga matsayi na shida zuwa na biyu da maki bakwai, bayan da ta karbi bakuncin Mainz ta kuma wulakantata da ci 6-1, a yayin da Wolfsburg ke a matsayi na uku da maki bakwai. Dortmund wacce ta yi raggon kaya a lokacin da ta je bakunci a birnin Berlin inda ta sha kashi da ci 3-1 a gaban Union Berlin ta sauka daga tebirin na Bundesliga zuwa matsayi na biyar da maki shida.