1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikicin kabilanci ya kunno kai a kasar Habasha

December 15, 2018

Rigingimu na kara muni tsakanin kabilar Oromo da wasu kabilun, tun lokacin da Firaminista Aby Ahmed wanda dan Oromon ne ya kama mulki.

https://p.dw.com/p/3ABPs
Äthiopien Somalia Vertriebene Menschen
Hoto: DW/B. Girma

Akalla mutune 21 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 61 kuma suka jikkata, a wani fadan kabilanci da ya barke a kudancin kasar Habasha wato Ethiopia a wannan Asabar.

Kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ce wasu daruruwa daga cikin mazauna yankin na tserewa suna shiga kasar Kenya.

Fitintinu dai na kara muni ne tsakanin 'yan kabilar Oromo da kuma wasu kabilun, tun lokacin da Firaminista Aby Ahmed wanda dan Oromon ne ya kama mulki.

Ko a ranaikun Alhamis da Juma'a ma, an sami tashe-tashen hankula tsakanin wasu 'yan Somali da Oromon a yankin Molaye da ke kan iyaka da kasar Kenya.