1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani mahari ya kashe dan majalisa a Birtaniya

October 15, 2021

Wani matashi dauke da wuka, ya hallaka wani dan majalisar Birtaniya dan jam'iyyar Conservative ta Firaminista Boris Johnson. An kai harin ne a gabashin Ingila a yau Juma'a.

https://p.dw.com/p/41k6f
Leigh-on-Sea, UK | British Lawmaker Sir David Amess reportedly stabbed
Hoto: REUTERS

Dan majalisar nan da aka kai wa hari da wuka a Birtaniya, Sir David Amess, ya mutu.

Wani matashi dan shekaru 25 ne ya kai hari a kan dan majalisar mai shekaru 69 lokacin da yake ganawa da 'yan mazabarsa a wata majami'a.

'Yan sanda sun tabbatar da kama maharin, wanda suka ce shi kadai ne ya aikata wannan danyen aiki.

Dan majalisar wato Sir David Amess mai shekaru 69, dan jam'iyyar Conservative ne ta Firaminista Boris Johnson.

Shaidu sun ce maharin ya daba wa dan majalisar wuka ne a wurare da dama a jikinsa a majami'ar Methodist da ke a gabashin Ingila.

Tun cikin shekarar 1983 ne dai Sir David Amess yake majalisar dokokin na Birtaniya.