1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Yan sanda 3 sun mutu a yayin raba rikicin iyali

Ramatu Garba Baba
December 23, 2020

Wani magidanci ya halaka 'yan sanda 3 a yayin da suka yi kokarin sasanta rikici a tsakanin iyali a wani yankin da ke tsakiyar kasar Faransa. Mutumin mai shekaru 48 da haihuwa ya cinna wa gidan wuta bayan aikata kisan.

https://p.dw.com/p/3n891
Symbolbild Frankreich Paris Polizei
Hoto: GEOFFROY VAN DER HASSELT/AFP

Mutumin mai shekaru arbain da takwas da haihuwa ya harbe 'yan sanda uku har lahira a yayin da suka yi kokarin ceto wata da ake kyauta zaton matarsa ce daga hadarin da take ciki. Daga bisani ya cinna wa gidan wuta. Sai dai jami'an tsaron da aka tura sun yi nasarar ceto matar.

Masu shigar da kara sun sheda ma kamfanin yada labaran Faransan na AFP cewa, akwai dan sanda guda da ya ji rauni wanda tuni aka ruga da shi asibiti. Babu dai cikakken bayani kan mutumin amma hukumomi suna sane da shi bisa wata kararsa da aka shigar a game da jayayyar da yake, mai nasaba da izinin kulawa da yara.