Wani kwamiti ya yi tir da MDD kan biris da zargin fyade | Labarai | DW | 17.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani kwamiti ya yi tir da MDD kan biris da zargin fyade

Wani kwamiti mai zaman kansa ya yi kakkausan suka kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi rikon sakarnar kashi kan ayyukan fyade da ake zaton dakarun wanzar da zaman lafiya sun aikata a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

A kalla dai a kwai sojojin Faransa 13 kana biyu daga Equatorial Guinea a yayin da uku 'yan kasar Chadi ne ke da alaka da cin zarafin kana nan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2014 a cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniyar a watan Afrilu.

A binkicen kwamitin na mutane uku sun yi kakkausan suka ga yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kan zarge-zargen tare da sukar lamirin wasu manyan jami'an hukumar bisa gazawa domin daukar matakin da ya dace.