1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jana'izzar 'yan matan da suka mutu a Kabul

Abdoulaye Mamane Amadou
May 9, 2021

A Birnin Kabul na Afghanistan, an yi jana'izar 'yan mata 'yan makarantar 50 da suka gamu da ajalinsu sakamakon fashewar bama-bamai a unguwar mabiya mazhabar Shi'a.

https://p.dw.com/p/3tAJf
Afghanistan Bombenanschläge auf Schule in Kabul
Hoto: Haroon Sabawoon/AA/picture alliance

Rahotanni sun ce dangi da iyayen yara 'yan makaranta da suka mutu na ci gaba da kasancewa cikin dimuwa, bisa harin da ya halaka daliban, wanda kuma ke zaman irinsa mafi muni da aka kaddamar kasa da shekara guda kan wata makaranta a kasar Afghanistan.

Baya da 'yan mata da suka mutu, wasu fiye da 100 suka jikkata sakamakon wasu tagwayen fashewar bama-bamai a makarantar Sayyedil Shuhada da ke unguwar mabiya mazhabar Shi'a ta binin Kabul.

Tuni dai hukumomi a kasar ta Afghanistan suka zargi kungiyar Taliban da wannan aika-aikar.