Wani dan kasar Amirka ya mutu a rigingimun Masar | Labarai | DW | 29.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani dan kasar Amirka ya mutu a rigingimun Masar

Taho mu gama tsakanin magoya bayan shugaban Masar da na 'yan adawa ya haddasa mace-mace da samun rauni da dama a sassa daban-daban na kasar.

Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu a birnin Alexandiriya na Masar yayin da wasu da dama kuma suka jikata lokacin wata arangama tsakanin wadanda ke adawa da manufofin shugaba Mohammed Mursi da kuma magoya bayansa. Ma'aikatar tsaron Amirka ta tabbatar da cewa wani sojanta daya mai shekaru 21 da haihuwa na daga cikin wadanda suka kwanta dama. Kana ta gargadi Amirkawa da su guji yin balagaro a kasar Masar sakamakon rashin kwanciyar hankali.

Dubban mutane ne dai suka gudanar da jerin zanga-zangogi a birane da dama na Masar ciki kuwa har da Alkahira domin walau nuna goyon baya ga shugaba Mursi ko kuma yin tofin Allah tsine ga irin salo na shugabancinsa. Wadanda ke adawa da manufofin shugaban na Masar sun lashi takobin gudanar da wata zanga-zangar kin jinin gwamnati a ranar Lahadi idan Allah Ya yarda. Babban burin da suka sa a gaba shi ne tailasta wa Mursi gudanar da zaben gaba da wa'adi, saboda rashin gani a kasa da ba su yi ba shekaru biyu bayan juyin-juya hali da suka yi, wanda ya kawar da Hosni Mubarak daga kujerar mulkin kasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal