Waiwaye kan wasanni da suka gudana a 2018 | Zamantakewa | DW | 31.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Waiwaye kan wasanni da suka gudana a 2018

Kofin duniya na kwallon kafa da ya gudana a Rasha na daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a 2018. Yayin da 'yan matan Najeriya suka lashe kofin kwallon kafar mata da ya gudana a Ghana.

Daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankali a wannan shekara mai karewa ta 2018, na zama gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya da kasar Rasha ta dauki nauyi inda kasar Faransa ta samu nasara. Dan wasan baya na kasar Jamus da kungiyar Bayern Munich, Jerome Boateng ya ce lallai wannan shekara ta 2018 ta zama mau tsauri ga 'yan wasan kasar. Jerome Boateng ya wallafa a shafinsa na zumunta na Instagram cewa fitar da Jamus daga wasannin rukuni na wasannin neman cin kofin kwallon kafa na duniya ya zama wani mawuyacin hali a tsawon wasannin rayuwarsa.

Daga wannan Litinin muke ban-kwana da wannan shekara ta 2018 miladiyya, inda za mu shiga sabuwar shekara ta 2019,  abubuwa ake ganin sun dauki hankali a fagen wasan kwallon kafa a Najeriya, shi ne rashin taka rawar gani a gasar kofin duniya na kwallon. Sai dai 'yan mata na babbar kungiyar kwallon kafar ta Najeriya su lashe kofin kwallon mata.

 Serena Williams shahararriyar 'yar wasan Tennis ta samu nasara a wasan da ya wakana a birnin Perth na kasar Australiya a wannan Litinin makonni biyu kafin fara babbar gasa ta farko mai muhimmanci na Tennis na shekara mai kamawa ta 2019. Wlilliams 'yar shekaru 37 da haihuwa daga Amirka ta samu nasara kan Maria Sakkari 'yar kasar Girka a zagaywen farko 7-6 ,7-3, 6-2.

Sauti da bidiyo akan labarin