1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wainar da aka toya a gasar Bundesliga

Ahmed Salisu RGB
September 13, 2021

Shirin ya duba irin wainar da aka toya a gasar Bundesliga ta tarayyar Jamus musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Mainz ta bi Hoffenheim har gida kana ta yi mata dukan kawo wuka.

https://p.dw.com/p/40GQo
Bundesliga | TSG Hoffenheim v 1. FSV Mainz 05
Hoto: Alex Grimm/Getty Images

A cikin shirin namu na wannan makon za a ji rin wainar da aka toya a gasar gasar Bundesliga ta tarayyar Jamus musamman ma irin yadda kungiyar kwallon kafa ta Mainz ta bi Hoffenheim har gida kana ta yi mata duka kawo wuka.

A gasar Firimiyar Ingila ma dai wasanni aka yi masu kayatar ciki kuwa har da haskakawar da Manchester United ta yi bayan da Christiano Ronaldo ko CR7 ya zura kwallaye har biyu a wasansa na farko bayan komawa Old Trafford. Batun da wasu ke ganin zai iya haifar da sauyi a gasar. Za kuma mu je Jamhuriyar Nijar don kawo muku cikikkan labarina bude gasar cin kofin-kofina ta kwallon kafa ta lokacin babban hutun shekara da daliban kasar kan yi.

A karshen mako aka buga wasannin mako na 4 na gasar Bundesliga a kakar bana. Guda daga cikin wasannin da ya ja hankalin ma'abota wannan gasa shi ne wanda aka yi tsakanin Hofenheim da Mainz inda mai masauki baki wato Hoffenheim ta sha kashi a hannun Mainz da ci biyu da nema, inda Jonathan Burkardt ya jefa kwallon farko da mintuna 20 da fara wasa.

Gabannin tafiya hutun rabin lokaci Hoffenheim ta yi ta kokarin farke kwallo amma ba ta samu nasara ba. Haka wasan ya ci gaba da gudana har zuwa minti na 77 inda Marcus Ingvarsten ya jefa wa Mainz kwallonta na biyu 'yan mintuna kalilan bayan da aka sanyo shi cikin wasan.

Idan muka dubi sauran wasannin na Bundesliga ma, a iya cewa an samu wasannin da suka kayatar inda Dortmund da Leverkusen suka tashi 4 da 3 a BayArena. Yayin da Munich ta lallasa Leipzig da ci 4 da 1 a Red Bull Arena. Yanzu haka dai Wolfsburg ce ke jan ragama a teburin na Bundesliga da maki 12 a wasanni 4 sai Munich mai maki 10 yayin da Dortmund ta ke a mataki na 3 da maki 9.

Daga Jamus bari kuma mu leka Birtaniya inda a jiya Lahadi Mohammed Salah na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya zura kwallo 100 A gasar Firimiya bayan karawar da suka yi da kungiyar kwallon kafa ta Leeds United. Salah ya jefa kwallon ne da minti na 20 da fara wasa. Yanzu haka dai ya shiga sahun wadanda suka yi bajinta ta jefa kwallo 100 ko fiye da haka a gasar ta Firimiyar Ingila. Wasu daga cikin wadanda suka taka irin wannan rawa sun hada da Alan Shearer da Harry Kane da Sergio Aguero da kuma Thierry Henry.

Christiano Ronaldo | Manchester United Player Mural | Old Trafford Stadium
Kamun ludayin Ronaldo Hoto: Martin Rickett/empics/picture alliance

To baya ga wannan bajinta ta Salaha, wani abu har wa yau da ke daukar hankali a gasar ta Firimiyar Ingila shi ne fara taka leda da Christiano Ronaldo ya yi bayan komawarsa Old Trafford inda har ya samu nasarar jefa kwallaye biyu a wasan da suka yi da Newcastle. Tuni dai masu sanya idanu kan irin wainar da ake toyawa a gasar ta Firimiya suka fara tsokaci kan irin sauyin da komawar Ronaldo taka leda ka iya yi a kakar bana.

To daga Ingila bari kuma mu nufi Jamhuriyar Nijar inda aka bude babbar gasar cin kofin-kofina ta kwallon kafa ta lokacin babban hotun shekara. Gasar wacce ta hada kungiyoyi 16 wadanda suka lashe kofin unguwanninsu na da burin zakulo sabbin matasan shahararrun 'yan kwallo da zummar ba su damar shiga manyan kulub na kasa don ci gaba da taka leda a babar gasa ta lig ta kasar ta Nijar.

Daga wasan kwallon kafa bari kuma mu mayar da hankali kan wasan Tennis musamman ma dai gasar US Open da ta mata inda Emma Raducanu ta kasar Birtaniya ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta lallasa abokiyar hamayara Leylah Annie Fernandez ta kasar Kanada.