1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka mutu a Italiya sun karu

August 15, 2018

Masu aikin ceto a Italiya na can suna suna koakrin zakulo wadanda hadarin wata gada ya rutsa da su a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/33BHO
Italien A10 Autobahnbrücke Morandi in Genua eingestürzt
Hoto: Reuters/S. Rellandini

'Yan sandan kasar ta Italiya sun ce akalla mutum 30 ne suka mutu, lokacin da babbar gadar da ke birnin Genoa ta rushe sakamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka.

Motoci masu yawa ne dai suka fada daga tsawon mita 100 suka kuma sauka kan hanyar jirgin kasa da ke karkashin gadar.

Jami'an kwana-kwana na amfani da karnuka na musamman, don nemo mutane da ke sauran motsi ya zuwa wayewar garin wannan Laraba.

An dai yi ta jin kukan mutane da ke neman dauki, a karkashin buraguzai.