1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta nuna goyon baya ga madugun adawa

Ramatu Garba Baba
February 3, 2019

Kasashen Tarayyar Turai 7 sun baiyana anniyarsu ta amincewa da madugun adawa Juan Guaido a matsayin shugaban kasa da zarar wa'adin da aka gindaya wa Shugaba Nicolas Maduro ya cika a wannan Lahadin.

https://p.dw.com/p/3CdBY
Venezuela NEU Protest & Demonstration gegen Nicolas Maduro in Caracas
Hoto: Getty Images/AFP/F. Parra

Shugaba Maduro a yayin ganawa da magoya bayansa a jiya Asabar, ya yi fatali da bukatar kasashen na kasashen Turai da suka hada da Jamus da Faransa da Birtaniya da Spaniya da Portugal da kuma Netherland da Beljium, ya jaddadawa magoyansa cewa shi ne zabbaben shugaban kasar Venezuela na gaskiya.

A daya bangaren kuwa madugun adawan, Guaido da ya jagoranci gangamin da aka gudanar a birnin Caracas, ya fadawa dandazon magoya bayansa, da kada su yi kasa a guiwa da su jajirce har sai sun kwatarwa kansu 'yanci daga kuncin da gwamnatin Maduro ta jefa su. Ya ce ba gudu ba- ja da baya, har sai an samar da gwamnatin riko da kuma gudanar da sabon zabe bisa tafarki na demokradiyya.

Amakon jiya ne madugun adawan ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko, inda nan take ya sami goyon bayan wasu manyan kasashen duniya, Amirka na daga cikinsu inda ta shawarci rundunar sojin kasar da ta amince ta mara masa baya.