Vatican ta gayyaci shugaban Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 03.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Vatican ta gayyaci shugaban Sudan ta Kudu

Fadar Vatican ta bayyana cewa ta gayyaci jagororin kasar Sudan ta Kudu, Shugaba Salva Kiir da jagoran adawa Riek Machar don halartar wani zama "na ibada" da tsarkake zukata.

Mai magana da yawun fadar ta Vatican Alessandro Gisotti ya bayyana cewa sun shirya a mako mai zuwa gayyatar shugabannin don samun nutsuwa cikin bautar ubangiji, a fito a motsa zukata don samun kusanci.

Wannan jawabi na zuwa bayan da Shugaba Kiir a watan Maris ya samu tarba ta musamman daga Fafaroma Francis a fadar ta Vatican inda anan ne ma Fafaroma ya nunar da sha'awar ziyartar kasar da ke yankin gabashin Afirka wacce ta sha fama da tashe-tashen hankula.