1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi von der Leyen a matsayin shugabar hukumar EU

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
July 16, 2019

Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta zabi Ursula von der Leyen ministar tsaron Tarayyar Jamus a matsayin sabuwar shugabar hukumar zartaswar kungiyar EU a yayin wani zaman majalisar da ta gudanar a ranar Talata. 

https://p.dw.com/p/3MAgS
Frankreich Wahl zur EU-Kommissionspräsidentin | Ursula von der Leyen
Hoto: Reuters/V. Kessler

Da gagarumin rinjaye na kuri'u  383 ne 'yan majalisar na kungiyar Tarayyar Turai ta EU suka zabi Ursula von der Leyen da shi, zaben da zai kai ta ga maye gurbin tsohon shugaban hukumar zartaswar kungiyar Jean-Claude Juncker. 
A wani dan takaitaccen jawabinta Ursula von der Leyen da ke zama ministar tsaron Jamus, ta gode wa wadanda suka jefa mata kuri’ar tare da jaddada matsayinta na ci gaba da aiki tukuru domin hadin kan Tarayyar Turai.

Von der Leyen na a matsayin macce ta farko da za ta rike mukamanin shugabancin hukumar kungiyar ta EU a daidai lokacin da kungiyar ke fama da wasu tarin kalubalai ciki har da batun ficewar Birtaniya daga kungiyar, batun da Ursula von der Leyen ta ce za ta bai wa Birtaniyar jalalo, kana kuma za ta kara maida hankali game da batun kare muhalli da dimamar yanayi a nahiyar ta Turai.