UNICEF: Yara da dama na gudun hijira | Siyasa | DW | 07.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

UNICEF: Yara da dama na gudun hijira

Wani rahoto da Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna irin kuncin rayuwa da yara kanana ke fuskanta, inda yanzu haka miliyoyi ke warwatse a duniya da sunan ‘yan gudun hijira.

A cewar asusun na UNICEF yake-yake da talauci da sauran tashe-tashen hankula, a yanzu, barazanar da suke yi a kan yara kanana ta kai kololuwa. Ted Chaiban shi ne daraktan tsare-tsare na asusun na UNICEF ya kuma ce:

"A yanzu haka yara kimanin miliyan 50 ke watangaririya, daga cikinsu miliyan 28 sun yi hijira ne bisa fadace-fadace da tashe-tashen hankula da kuma talauci wansunsu na kan gararamba don neman sake hadewa da iyayensu"

A cewar asusun UNICEF akwai bukatar a fahimci cewa yaran da suka rasa mahalli makomarsu ba karamar barazana ba ce, kuma kamata ya yi su kansu iyayen yaran a ba su kula ta musamman. Don haka akwai kalu bale mai yawa bisa kula da yaran da ke gudun hijira. A yanzu haka idan dai aka ambaci 'yan gudun hijira dole a yi batun kasar Iraki, kasar da ke cikin tashin hankali tun shekara ta 2003 a lokacin da Amirka da kawayenta suka kai hari a nufin kifar da gwamnatin Saddam Husseini. Abin da kuma ya kawo a yanzu Iraki ke kan gaba wajen yawan ‘yan gudun hijira. Maulid Warfa jami’ine a ofishin UNICEF da ke kasar Iraki ga kuma abin da yake cewa:

"Ilimi da kai farmaki su ne manyan kalubale a Iraki yanzu haka. Shi ne kuma dalilin da ya sa duk inda muka je za ka ga kalubale, bisa yadda yara ke gararamba, domin ba su da wani abin yi. Makomar yaran Iraki tana cikin mummunar tsaka mai wuya."

A yanzu haka dai bisa yadda matsalar yara ta ke neman fin karfin kungiyoyi ba da agaji kamar UNICEF, nauyi ne kan duk wanda zai iya ba da gudumawa domin tallafa wa yaran a duk inda aka ga za’a iya. Kamar dai yadda Ted Chaiban daraktan tsare-tsare na asusun na UNICEF ya bayyana. Rohoton dai ya kara jaddada irin yadda karuwar ‘yan gudun hijira ke yi a duniya, kana ya nunar da cewa tashe-tashen hankula ba bangaren da ba su shafa, kama daga tattalin arziki da kuma tarwatsa manya da yara, abin da kuma a wasu lokutan kan shafi kasashen da ba sa cikin tashin hankalin.

 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin