Umarnin dakatar da fada da ′yan tawaye a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 28.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Umarnin dakatar da fada da 'yan tawaye a Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bada umarni ga sojojin kasar da su dakatar da duk wani fada tsakaninsu da 'yan tawaye a wani mataki na mutunta yarjejeniya.

Shugaban ya bada wannan umarni ne cikin wani kudri da ya dauka a ranar Alhamis, wanda kuma tuni ya fara aiki daga wannan Jumma'a a cewar Ateny Wek kakakin fadar shugaban kasar a wani mataki na kawo karshen yakin da ya daidaita wannan kasa tsawon watanni 20 da suka gabata. Yarjejeniyar dai ta tilasta tsagaita wuta kwanaki uku bayan rattaba hannun kowane bengare, wanda a baya ma an sha yin hakan amma kuma kwanaki kalilan yarjejeniyar ta fada ruwa. Kakakin fadar shugaban kasar ta Sudan ta Kudu ya ce a halin yanzu dai suna jira su ga Riik Masha ya dauki irin wannan mataki ga mayakansa. Amma kuma babbar ayar tambayar a nan ita ce, wane fada a ji shi Riik Mashar yake da shi ga mayaka 'yan tawayen?