1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar shugaban Ukraine ta samu rinjaye a zaben majalisa

Abdoulaye Mamane Amadou
July 22, 2019

Sakamakon zaben 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a kasar Ukraine ya yi nuni da cewar jam'iyyar sabon shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ce ke kan gaba da gagarumin rinjaye.

https://p.dw.com/p/3MTaE
Ukraine | Parlamentswahlen | Wolodymyr Selenskyi
Hoto: Reuters/V. Ogirenko

Jam'iyyar sabon shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ta samu gagarumin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a yau Lahadi inda ta tashi da kishi 43.9 ciki dari na adadin kuri'un da aka jefa, lamarin da ke tabbatar da hasashen jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar a baya.

Ko baya ga jam'iyyar sabon shugaban wasu jam'iyyun siyasa hudu na iya kai gaci da kashi biyar cikin dari na adadin da yake wajibi ga jam'iyyar siyasa kafin samun damar shiga majalisar ta dokoki kamar yadda wani binciken na jin ra'ayin jama'ar kasar da wasu kungiyoyi uku suka tabbatar.