1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zalensky ya sallami wasu manyan jami'ai

January 24, 2023

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sallami wasu manyan jami'an gwamnati saboda cin hanci da rashawa

https://p.dw.com/p/4MdN0
Ukraine Kiew | Wolodymyr Selenskyj
Hoto: President of Ukraine/apaimages/IMAGO

Mukaddashin ministan tsaro da mataimakin babban jami'i a fadar shugaban kasar Ukraine sun ajiye aikinsu sakamakon badakalar cin hanci da rashawa.

Ajiye aikin manyan jami'an ya zo ne jim kadan bayan da shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelensky ya  sanar da wasu sauye-sauye a cikin manyan jami'an gwamnatin kan zargin cin hanci da rashawa tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar kasar.